An yi zanga-zangar kin jinin APC a Katsina (Hotuna)

An yi zanga-zangar kin jinin APC a Katsina (Hotuna)

Daruruwan magoya bayan dan majalisar wakillai mai wakiltar Malumfashi da Kafur Honarable Babangida Ibrahim wanda aka fi sani da Talu suka yi wa babbar hedikwatar jam'iyyar APC dake cikin birnin Katsina don nuna fushin su da kin amincewa da korar dan majalisar nasu da jam'iyyar tayi.

An yi zanga-zangar kin jinin APC a Katsina (Hotuna)
An yi zanga-zangar kin jinin APC a Katsina (Hotuna)

Shi dai Honarable Babangida jam'iyyar ta fitar da sanarwar korar shi ne dai a makon da ya gabata.

Matasan da suka hada da mata da maza sun yi ta rera wakokin kin jinin jam'iyyar da kuma matakin da ta dauka kan dan majalisar tasu tare kuma da daga kwalaye dauke da bayanai da dama.

Daga karshen zanga-zangar kuma shugabannin matasan sun mika koken su a rubuce ga shugabannin jam'iyyar APC din da suka tarbe su.

KU KARANTA: Masari na so ya kashe ni - Shema

A wani labarin kuma, Jam’iyyar PDP ta ce za ta yi maja da wadansu jam’iyyu bakwai kafin tunkaran zaben 2017.

Tsohon ministan watsa labarai Jerry Gana ne ya sanar da hakan ne da yake mika rahoton kwamitinsa da uwar jam’iyyar ta nafa domin bata shawarwari akan hanyoyin da za ta bi domin warware matsalolin da ta ke fama da su yanzu.

Jery Gana yace jam’iyyar na tattaunawa da wadansu jam’iyyu a kasa Najeriya domin yin maja kafin zaben 2019.

Tsohon ministan ya ce yana da tabbacin cewa jam’iyar APC ba za ta kai labari ba a zaben 2019 musamman ganin irin shirin da jam’iyyarsa ta ke yi domin tunkarar 2019.

Ya kuma karyata jita jitan da ake ta yada wa wai jam’iyar PDP za ta canza suna bayan tayi maja da wadansu jam’iyyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel