Hakkin maza ne su gamsar da matayen su, sabo ne idan basuyi ba – Sheikh Al-Yolawi

Hakkin maza ne su gamsar da matayen su, sabo ne idan basuyi ba – Sheikh Al-Yolawi

- Wani babban limami a Abuja yayi kira ga mazaje da su girmama da kuma gamsar da matan su

- Limimim yace wadanda ke take hakkin matansu ta fannin auratayya masu sabo ne sosai kuma Allah zai hukunta su

Maza wanda suke take hakkin matansu ta fannin auratayya zasu fuskanci azaban Ubangiji bisa ga wani darasi da babban limamin Area 10, Sheikh Yahya Al-Yolawi yayi.

A ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairu, Sheik din ya shawarci maza masu aure da su gamsar da matansu ta fannin auratayya don kare matan daga cin amana.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Al-Yolawi ya bayar da shawaran ne a lokacin hudubar sa na sllar Juma’a mai taken “Hakkin maza da mata a musulunci.”

Hakkin maza ne su gamsar da matayen su, sabo ne idan basuyi ba – Sheikh Al-Yolawi

Al-Yolawi said there are men who do not satisfy the sexual needs of their wives and that: “Such people are great sinners and will be convicted in the sight of Allah.

KU KARANTA KUMA: An kama matar aure tana cikin aikata masha’a tare da aminin mijinta (HOTUNA)

Al-Yolawi yace akwai maza da basa gamsar da matansu ta fannin auratayya kuma cewa “Irin wadannan mutane sun kasance masu mummunan sabo kuma Allah zai hukunta su.

“Hakkin maza ne su gamsar da matansu ta fannin jima’I saboda karda su fada halaka ta hanyan hangen wasu mazajen don kashe kishir ruwansu.

“Allah mai girma yaba mata daman Tarayya da mazansu.

Malamin ya kalubalanci maza da su girmama matansu kuma karda su yaba kyawun wasu mata a gaban matansu.

“Wannan na iya haddasa kishi da kuma zargi a zukatan mata. Zatayi tunanin cewa mijinta na soyayya da wannan matar ne.

“Wannan tunanin guba ne dake kashe aure kuma ya zama dole a kore shi.”

Al-Yolawi ya kuma shawarci maza da mata da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya a gida.

Yace fushin miji babu abunda yake haddasa wa ga mata sai tashin hankali, bakin ciki da kuma dorewan kai, ya kara da cewa fushin mata baya kawo komai ga namiji sai dana sani.

Malamin ya shawarci ma’aurata da su kasance masu hakuri da tausayi a al’amuransu kuma ya bukaci maza da su nuna cikakken yardansu a kan matan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel