Hukumar EFCC zata gurfanar da barayin mai 12 a Neja Delta

Hukumar EFCC zata gurfanar da barayin mai 12 a Neja Delta

- Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa zata gurfanar da barayin man fetur 12 a Fatakwal, jihar Ribas

- Rundunar sojin ruwa ne tayi ram da su kuma ta mika su ga hukumar EFCC

- Idan ta gama bincike, zata gurfanar da su a kotu

Hukumar EFCC zata gurfanar da barayin mai 12 a Neja Delta
Hukumar EFCC zata gurfanar da barayin mai 12 a Neja Delta

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa zata gurfanar da barayin man fetur 12 da rundunar sojin ruwa ta kama a Fatakwal, jihar Ribas.

Wannan na faruwa ne bayan rundunar sojin ruwan tayi kaca-kaca da matatun man gargajiya 40 kuma ta damke barayi a Jones Creek, karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta.

KU KARANTA: Ayi wa shugaba Buhari addu'a

An damke su ne ranan Alhamis bayan an gano matatun man 40 wanda ya kunshi ton mai miliyan 1.

An damke barayin 12 a Fatakwal da randan MV OMISAN 1mai lamban IMO 7216244, da kwale-kwaln ruwa biyu, a Rumuolumeni da Fatakwal.

Kwamandan rundunar sojin ruwa Commodore W.O. kayoda, ya mika su ga hukumar EFCC domin bincike.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel