Boko Haram sun hallaka sabbin soji 7, sunyi garkuwa da macen soja 1

Boko Haram sun hallaka sabbin soji 7, sunyi garkuwa da macen soja 1

Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram ta kai wata sabon hari kan wasu sabbin soji a Maiduguri, inda ta hallaka mutane 7 kuma sukayi garkuwa da wata macen soja guda 1.

Boko Haram sun hallaka sabbin soji 7, sunyi garkuwa da macen soja 1
Boko Haram sun hallaka sabbin soji 7, sunyi garkuwa da macen soja 1

Game da cewar Washington Post, an kai harin ne da yammacin ranan Alhamis, 9 ga watan Febrairu, kusa da garin Mafa a Maidugurin jihar Borno.

KU KARANTA: An maka shugaba Buhari a kotu

Wani soja wanda aka sakaye sunansa ya tabbatar da wannan labara. Amma har yanzu dai ba’a samu daman tabbatar da wannan labari daga bakin kakakin hukumar soji ba saboda yaki yin Magana.

Boko Haram bata daina kai hare-hare kan soji ba duk da cewan an fitittikesu daga cikin dajin Sambisa a Disamban shekaran 2016.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel