Bayan Jammeh yayi mata kar-kaf, EU zata tallafawa Gambia da €75m

Bayan Jammeh yayi mata kar-kaf, EU zata tallafawa Gambia da €75m

Kungiyar tarayyar turai, EU, ta yi alkawarin bawa kasar Gambia euro miliyan 75 a matsayin tallafi.

Matakin yana a matsayin sabunta taimakon da kungiyar tarayyar tura ke bawa Gambian a baya, makwanni kadan bayan ficewar tsohon shugaba Yahya Jammeh.

Bayan Jammeh yayi mata kar-kaf, EU zata tallafawa Gambia da €75m
Bayan Jammeh yayi mata kar-kaf, EU zata tallafawa Gambia da €75m

A shekara ta 2014 tarayyar turan ta dauki matakin janye tallafin da take bawa kasar, sakamakon haramta alaka ko auren jinsi guda a waccan lokacin.

Jim kadan bayan kammala taron da yayi da shugaba Adama Barrow, Kwamishinan sashin lura da kyautata cigaban alakar kungiyar tarayyar turan da kasashen duniya, Neven Mimica, ya ce za’ayi amfani da tallafin kudin wajen bunkasa noma, gina hanyoyi, da kuma samar da ayyukan yi a Gambia.

KU KARANTA: Yan matan jami'ar Legas sun yi tsokaci game da hana su sa matsatssun kaya

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya ta ce ta karbe ikon kamfanin jiragen sama na Arik wanda ke fama da bashi mai dumbin yawa da ke neman durkusar da kamfanin.

An kwashe tsawon lokaci kamfanin Arik, wanda ke daukar nauyin kashi 55 cikin 100 na matafiya a kasar, yana fama da kalubale da dama.

Kamfanin yana ta fuskantar tangarda sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da matsaloli wajen gudanar da ayyukansa da rashin biyan ma'aikatansa albashi da kuma dumbin bashi da ake bin sa.

Wadannan matsaloli ne suka sa hukumomin kasar suka shiga tsakani domin shawo kan al'amarin saboda kar kamfanin ya rushe.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel