An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha

An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha

Idan mai karatu bai manta ba, a jiya Legit.ng ta kawo muku labarin wani gurgu da Sojoji suka tumurmushe shi a garin Onitsha na jihar Anambra kan ya sanya khakin Soja, inda har ma muka kawo muku bidiyon lamarin.

An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha
An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha

To a yau an gano inda wannan gurgun yake, hakan kuwa ya faru ne bayan wata cibiyar bada tallafi ga marasa karfi mai suna The Kokun foundation tayi alkawarin bada N20,000 ga duk wanda ya gano mata inda gurgun nan yake domin ta tallafa mai.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta cafke sojojin da suka tumurmusa wani gurgu

Cikin cigiyar da cibiyar ta bayar tace : “muna sanar muku da cewar mun gano inda wannan gurgun da sojoji suka tozarta a garin Onitsha yake, don haka mun fara gudanar da shirin tallafa masa da matsuguni da kuma tallafin kudi.

An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha
An gano gurgun da Sojoji suka tumurmusa a garin Onitsha

“jama’a mu sanu muna zamanin dimukradiya ne ba mulkin soja ba, don haka aikin mu shine kawar da talauci, yunwa da fatara a kasar nan. zamu cigaba da baku rahoton ayyukan mu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga dai bidiyon cimiymiyan da sojoji suka yi ma wannan gurgu:

Asali: Legit.ng

Online view pixel