Shugaba Buhari na bukatar Adu’a ‘yan Najeriya

Shugaba Buhari na bukatar Adu’a ‘yan Najeriya

- Gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya bukaci duk ‘yan Najeraya taya shugaba Buhari addu’a.

- Gwamnan ya ce mutanen arewa maso gabas sun fi bukatar lafiyar Buhari saboda kokarin durkushe Boko Haram.

Shugaba Buhari na bukatar Adu’a ‘yan Najeriya
Shugaba Buhari na bukatar Adu’a ‘yan Najeriya

Gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya shawarci shugabannin addinai a Najeriya cewa su taya shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a na samu lafiya.

Tun da shugaban kasa ya yi tafiya ana maganganu game da lafiyar shugaban daga fadar shugaban kasa da kuma jami'an gwamnati.

Jaridar News Agency ta Nigeria (NAN) ta rawaito cewa Bindow ya yi wannan bayyani ne a ranar Laraba, 8 Fabrairu, 2017 a lokacin da gwamnan ya karbi bakonci mutanen karamar hukumar shelleng a Yola babban birnin jihar Adamawa.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Kalli sabuwar hoton Shugaba Buhari da jiga-jigan jam'iyyar APC a garin Landan

A cewar Gwamnan, kiwon lafiya da yanayin shugaban kasa ya fi damuwar mutanen arewa maso gabas, saboda ganin kokarin da shugaban kasa ke yi na kawo karshen ‘yan ta’adda a yankin.

Ya ce ina roƙon dukan shugabannin addinai su shiriya wani adua’a na musamman domin samun lafiya shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin jawabin shugaban tawagar, wani tsohon Sanata, Hassan Barata, ya yaba wa gwamnan saboda gina wata hanya da ta hada Kiri zuwa Shelleng, ya kara da cewa hanya ya janyo hankalin yan zuba jari zuwa garin.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel