Mutane 6 da suka ba mu tabbacin cewa Buhari na raye

Mutane 6 da suka ba mu tabbacin cewa Buhari na raye

– Ana ta magana game da lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari

– Lai Mohammed yace Buhari na nan cikin koshin lafiya

– Bukola Saraki ma dai yace sun yi waya jiya

Mutane 6 da suka ba mu tabbacin cewa Buhari na raye
Mutane 6 da suka ba mu tabbacin cewa Buhari na raye

Yayin da ake ta surutu game da lafiyar shugaba Buhari, mun kawo maku jerin mutane 6 da su ka tabbatar da cewa shugaban kasar na nan garau.

Mukaddashi Osinbajo

A farkon makon nan Farfesa Osinbajo ya bayyanawa Duniya cewa ya gana da shugaba Muhammadu Buhari da kuma yadda suka yi.

Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa na kasa Bukola Saraki, yayi magana da shugaban kasar a wayar tarho jiya da dare. Saraki dai ya bayyana haka bayan sun gama zantawa da shugaban kasar.

KU KARANTA: Buhari na nan garau inji gwamnain tarayya

Hajiya Rakiya Adamu

‘Yar uwar Buhari Hajiya Rakiya wanda ita kadai ta rage masa a Duniya ta tabbatar mana da cewa Dan uwan na ta yana nan da ran sa don haka Jama’a su daina biyewa rade-radin kawai.

Hadi Sirika

Sanata Hada Sirika wanda shi ne Ministan sufurin jiragen sama kuma Dan uwan shugaban kasar ne ya tabbatar da cewa ya ma kai ziyara ga shugaban kasar a Landan yana kuma da ran sa.

Abu Ibrahim

Wani Sanatan Jihar Katsina inda shugaban kasar ya fito yace gajiya ce kurum ke damun shugaba Buhari amma ba rashin lafiya ba.

Minista Lai Mohammed

Ministan yada labarai na Najeriya ya fito yayi magana game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lai Mohammed ya musanya rade-radin da Jama’a ke ta yadawa a kasa game da shugaban a jiya.

Yau dinnan ne kuma manyan ‘Yan Jam’iyyar APC suka kai ziyara ga shugaban kasar a Birnnin Landan inda yake hutawa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel