Wata sabuwa: Makafi za su fito zanga-zanga a Kano

Wata sabuwa: Makafi za su fito zanga-zanga a Kano

- Makafi a jihar Kano sun sha alwashin fitowa kwansu da kwarkwata don yin zanga-zanga na sai baba-ta-gani in har gwamnati biya musu bukatunsu ba

- Hakan ana ganin ba zai rasa nasaba da matsin tattalin arziki ba ganin cewa gwamantin jihar ta matsa da kamen masu bara ta kuma gaza biyansu alwus din ta yi alakawari ba

Makaf

Wata sabuwa: Makafi za su fito zanga-zanga a Kano
Wata sabuwa: Makafi za su fito zanga-zanga a Kano

i a jihar Kano sun yi alkawarin gudananar da wata gagarumar zanga-zanga a jihar a inda za su yi fitowar farin dango in har gwmantin jihar ba ta dubu lamarinsu ba.

A wani shirin Rediyo mai suna Inda ranka wanda wani gidan rediyo mai zaman kansa ya ke gudanarwa a jihar ya ce, makafin sun hassala ne dangane halayyar gwamnatin na watsi da lamarinsu, baya ga matsanacin takurawa rayuwarsu da jami'anta ke yi na kama su a duk lokacin da suka fita bara.

Baya ga cewa gwamnatin ta yi alkawarin tallafawa rayuwarsu da biyansu alawus-alawus a karshen kowanne wata amma hakan a yanzu ya fasakara.

Rahoton bai fadi lokacin da makafin za su gudanar da zanga-zangar ba bai, bai kuma ji ta bakin hukumonin abin da ya shafa ba dangane da kokarfe-korafen na su.

Sai dai mai rahoton ya yi hira da wani Lauya kan batun hana bara da Makafin ke korafi a kai, ya kuma ce hana bara dokar gwamnati ce, kuma ba su da damar karya dokar, sai dai su garzaya domin su kalubalance ta.

Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar Hisbah, ta matsa kai mi wajen aiwatar da dokar da ta hana yin bara a jihar, a inda ta ke kama mabarata, tana kuma gurfanar da su gaban kuliya wanda hakan makafin ke ganin cewa takurawa rayuwarsu ce ganin yanayin da ake cikin na matsin tattalin arziki a kasar.

Aiko da naku ra'ayin dangane da wannan labarin a http://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel