Mutanen kasuwa sunyi wa barauniya zindir a bainar jama’a a jihar Legas

Mutanen kasuwa sunyi wa barauniya zindir a bainar jama’a a jihar Legas

Kwankin nan ne a jihar Legas, mutanen kasuwa su damke wata barauniya mai suna Jane Okeke yayinda take satan wasu kayayyaki a shagon PEP Super Store a Isolo, jihar Legas.

Mutanen kasuwa sunyi wa barauniya zindir a bainar jama’a a jihar Legas
Mutanen kasuwa sunyi wa barauniya zindir a bainar jama’a a jihar Legas

P.M.EXPRESS ta bayyana cewa, barauniyar ta shiga cikin dakin da akayiwa kwastamomi domin gwada kayan da zasu saya kafin su biya kudi. Amma, Jane Okeke ta zabi kaya daban-daban guda 11 sai ta shiga dakin da jakanta, tana wayancewa da gwada kayan kafin ta biya kudi.

KU KARANTA: Daliba ta hallaka a hadarin mota

Ashe Okeke na cire kayan da ke jikintane tana sanyawa cikin jaka kuma tana sanya sabbin kayan a madadin tsaffin. Yayinda ta kai kofar fita daga shagon, jami’in tsaron shagon ya bukaci bincikenta inda aka gano cewa ashe tana sanye da wasu sabbin kayan da tayi ikirarin zata saya.

An mika ta ga hukumar yan sanda.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel