Sarkin Zazzau ya nemi gafaran al'ummar masarautar Zariya

Sarkin Zazzau ya nemi gafaran al'ummar masarautar Zariya

Mai martaba sarkin Zazzaun, Alhaji Dakta Shehu Idris yayi roki al’ummar masarautansa gafara tare da neman afuwar duk wanda yayi ma ba daidai ba a yayin bikin cikar shekarunsa 42 akan karagar mulki.

Sarzin Zazzau ya nemi gafaran al'ummar masarautar Zariya
Sarzin Zazzau, Alh Shehu Idris

A yayin gudanar da addu’o’in godiya ga Ubangiji Allah da yayi ma Sarkin tsawon rai zuwa wannan shekaru, Sarkin ya nemi afuwar jama’a inda yace ba karamin baiwa bace Allah yayi ma mutum ya kwashe shekaru 42 yana mulki.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta cafke sojojin da suka tumurmusa wani gurgu

“A lokacin dana hau sarautan mulin zage zage, shekaru 39 ne a wancan lokaci. Amma a yau ina bikin cikar shekaru 42 akan karagar mulki, kaga wannan abin na gode ma Allah ne. don haka nake neman gafaran duk wanda na bata ma rai.

“Ina sake yin amfani da wannan dama na roki yan Najeriya da su cigaba da zaman lafiya da juna, don kuwa idan babu zaman lafiya, toh al’umma ba zata samu cigaba mai daurewa ba.”

Yayin dayake jawabi wakilin gwamna Nasir El-Rufai a taron, mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Yusuf Bala Bantex ya roki mai martaba Sarki daya rubuta cikakken tarihin rayuwarsa, don rayuwar tasa cike take da darussa ga yan baya.

Mutane kalilan ne ke da wayo a cikin mu a lokacin da ka zama Sarki, don haka jama’a zasu dauki darussa daga rayuwarka. Muna kara yi ma Allah godiya daya baka tsawon rai, kuma ka bada gudunmuwarka wajen kawo cigaba a kasa baki daya.

Da wannan ne muka kara rokon Allah daya tsawaita rayuwarka, tare da kara maka basira da hikima, ina so inyi amfani da wannan dama inyi maka albishir da cewa gwamnatin mu zata kammala ayyukan ruwan Zariya, sakamakon rashin ruwa na cikin manyan matsalolin da ake jama’a suke fuskanta.” Inji Bantex.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel