Wataƙila Buhari yawo dawo gida Najeriya ranar Asabar

Wataƙila Buhari yawo dawo gida Najeriya ranar Asabar

Alamu na cigaba da nuna yiwuwar dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Najeriya a ranar Asabar 11 ga watan Feburairu daga hutun daya tafi a kasar Ingila.

Wataƙila Buhari yawo dawo gida Najeriya ranar Asabar
Buhari a Landan

Wata majiya kakkarfa ta cikin gida ta shaida ma jaridar Leadership haka. Majiyar tace, “idan dai ba an canza shawara ba, muna sa ran dawowar shugaban kasa a cikin kwanakin karshen mako, musamman ranar Asabar.”

Jaridar ta binciko cewar a ranar Talatar data gaba ne shugaba Buhari ya soke shirin gudanar da hira ta musamman ga wata gidan jarida dake kasar waje, amma ana tsammanin zai yi hirar da wata jarida ta daban kafin satin nan ya kare.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta cafke sojojin da suka tumurmusa wani gurgu

Wata majiyar ta daban ta shaida mana cewar: “A yanzu haka shugaba Buhari ya kammala shirya jakunkunansa don shirin daowa gida ranar Lahadi, amma sai likitocinsa suka shawarce shi daya dakata har sai an fitar da sakamakon gwaje gwajen da aka yi masa.

“Ina tabbatar muku shugaba kasa zai iya cigaba da zama a ksar Landan sakamakon likitocins sun matsa masa akan lallai ya dakata da tafiyarsa, amma gaba daya hankalinsa na gida Najeriya.”

Dangane da jita jitan da ake yadawa na cewa shugaban na cikin halin rai fakwai-mutu fa kwai kuwa, majiyar ta ce, “kana mamakin jin haka daga mutanen mu ne? da ace shuwagabanninmu na baya ne suka fita ba tare da sanar da majalisa ba, da za zaka ji wannan surutan ba. Amma wannan shugaban namu ya dage akan lallai sai ya bi doka, kuma ba wannan bane karo na farko da ya fara fita kasar waje ai.”

Jaridar Leadership ta ruwaito kaakakin shugaban kasa Femi Adesina yana fadin cewar nan bada dadewa bane shugaba Buhari zai dawo.

Idan za’a iya tunawa, a ranar Lahadin data gabata ne shugaba Buhari ya aika ma majalisa da takardan inda a ciki yake sanar dasu zai tsawaita zamansa a kasar Ingila don ya jira ya amshi sakamakon gwaje gwajen da aka yi masa, kamar yadda likitocinsa suka bashi shawara.

A wani labarin kuma, ministan watsa labarai da al’adun gargajiya, Alh Lai Muhammed ya bayyana a jiya cewar abin dariya ace wasu su dinga kamanta tafiyar shugaba Buhari da na tsohon shugaba Yar’adua.

Muhammed ya bayyana haka ne bayan taron majalisar zartarwa wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa, wannan batu na Muhammed yazo ne kwanaki biyu bayan Osinbajo ya jaddada cewar shugaba Buhari ne kadai keda daman fitar da matsayin lafiyarsa.

Da aka tambaye shi ko shugaba Buhari na cikin koshin lafiya, Lai Muhammed yace “ina tabbatar muku cewar shugaba Buhari na cikin cikakken koshin lafiya, babu wata tantama. Amma kuna ganin shugaba Buhari zai shiga cikin halin rashin lafiya kuma ace muna nan muna gudanar da ayyukan mu kamar ba komai?

Wasu sun zarge ni akan na bukaci a dinga fitar da bayanin rashin lafiyar Umaru Yar’adua a duk sa’a, toh ina so in fada musu, babu wata kamanceceniya ko kada tsakanin shuwagabannin biyu, don kuwa Buhari ba a asibiti yake ba, lafiyarsa kalau.

Da aka sake tambayarsa kowa ya dace shugaba Buhari yayi tafiya alhalin ana cikin halin matsin tattalin arziki? Sai yace “sosai ma kuwa, shin shugaba Obama ba yaje hutu ba? Idan ya zama dole sai shugaban kasa ya tafi hutu, dole ne ya tafi hutu, kasan yawan ministocin da suka tafi hutu a shekarar nan?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel