A kullun ina magana da Buhari – yayar shugaban kasa

A kullun ina magana da Buhari – yayar shugaban kasa

Hajiya Rakiya wacce ta kasance yaya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa a kullun tana magana da shi kuma ta bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yi masa addu’an samun lafiya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa babban yayar shugaban kasar da ta rage masa tace yan Najeriya su janye daga yada jita-jitan mutuwar sa kamar yadda yake bukatar addu’oi daga ko dukkan yan Najeriya domin nasara gurin magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Masu zanga zanga na son bata sunan Buhari ne – kungiyar Buhari

Tace shugaban kasa na iya rashin lafiya ko ma ya mutu “a duk lokacin da mahallicinsa ya so”.

Tace shugaban kasar na cikin koshin lafiya kamar yadda take magana dashi a kai a kai tun bayan tafiyarsa birnin Landan.

A kullun ina magana da Buhari – yayar shugaban kasa
A kullun ina magana da Buhari – yayar shugaban kasa

“Dawowa ta daga umrah kenan kuma a lokacin da nake kasar Saudiya ina magana dashi a kullun.”

“Mu 28 ne a gurin mahaifiyarmu marigayiya Hajiya Zulaihatu wacce ta rasu a shekarar 1992, amma Buhari ne dan autanmu”.

Amadodo kamar yadda aka fi saninta tace tana magana dashi duk sa’oi goma.

Wani makusancin shugaban kasa, Alhaji Aminu Na-Dari ma ya yi magana a kan lamarin lafiyar shugaban kasa cewa yana magana da Buhari a kai a kai kuma cewa yana cikin koshin lafiya.

Yace matsalar koma bayan tattalin arziki da ake ciki a yanzu ba shugaba Buhari bane ya haddasa amma yana kokari sosai don ganin ya shawo kan al’amarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel