Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa

Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa

– Garin dadi na nesa, Dan wasa John Stones na Kungiyar kwallon Man City na ruwan kudi

– Tauraron dan wasan ya saye wani katafaren gida a Ingila

– Stones bai wuce shakau 22 a Duniya ba

Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa
Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa

Matashin dan wasan nan na Kungiyar Manchester City na Ingila na facaka da kudi kurum ba abin da ya dame sa. Sabon dan wasan na Kungiyar City ya saye wani makeken gida wanda abin ba a magana.

Stones duka-duka bai wuce shekaru 22 da haihuwa ba amma ya saye wani katafaren gida na Miliyan £3.4 watau a kudin Naira dai wannan gida zai haura Miliyan biyu. Kwanan nan dan wasan bayan ya koma Manchester da buga wasa bayan ya baro Kungiyar Everton.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya kai ziyara asibiti

Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa
Kudi na inda suke: Dan wasan Manchester City na wulakanci abin sa

A wannan katon gida da dan wasan ya saya akwai dai filin buga wasanni da kuma dan lambu ga kuma dakuna baja-baja. Stones dai ya shige cikin gidan tare da ‘yar sahibar sa watau Millie Savage.

Can kwanaki Tauraron dan wasan kwallon Kafa, Cristiano Ronaldo ya bude wani katafaren otel a Kauyen su na Funchal da ke Garin Madeira a Kasar Portugal. Otel din na dauke da dakuna 48, wadanda ake haya kowane dare kan EURO £180. Sannan a kowane daki akwai na’urar WIFI domin hawa shafin yanar izo. Ga manyan fitilu da kuma gidan wanka na zamani. Wayyo Allah.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel