An sace ‘Yan kasar waje a Neja-Delta

An sace ‘Yan kasar waje a Neja-Delta

– An sace wasu baki ‘Yan wata kasa a Najeriya

– Bakin da aka sace dai mutanen kasar Rasha ne da Kasar Ukraine

– Wannan abu ya faru ne a Yankin Neja Delta

An sace ‘Yan kasar waje a Neja-Delta
An sace ‘Yan kasar waje a Neja-Delta

Mun samu labari cewa an sace wasu baki ‘Yan kasar waje a cikin Najeriya. Wannan abin kunya dai ya faru ne a Yamkin Neja-Delta mai arzikin mai a kasar.

An dai sace har mutane 7 wadanda duk ‘Yan kasar Rasha ne sannan kuma da wani mutum guda tak dan kasar Ukraine mai makwabtaka da Rasha. ‘Yan fashin kan teku ne dai suka sace bakin a kusa da Garin Brass da ke Yankin Kudu-maso-Kudu na Kasar.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna ya ga ta kan sa

Kafar yada labarai na kasar Rasha mai suna TASS ta sanar da wannan labari. ‘Yan fashin kan tekun dai sun kai hari ne ga kirgin da ya kwaso ‘Yan kasar Rashan a wani Yanki mai arzikin mai. An yi musayar wuta tsakanin ‘yan fashin da masu gadin jirgin. Jami’an Soji dai ta maida martani kwakkwara game da harin.

Jiya kuma mu ka samu labarin cewa ‘Yan Majalisun Najeriya suna karar Gwamnatin kasar Amurka a Kotu inda suke neman gwamnatin kasar ta biya su kudi har dala biliyan $1. ‘Yan Majalisun sun ce Amurka tayi masu sharrin lalata da ‘yan mata.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel