Wasu basu son gaskiya, amma ba zan iya karya ba - Femi Adesina

Wasu basu son gaskiya, amma ba zan iya karya ba - Femi Adesina

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya rantse cewa ba zai taba yin karya ba ko da kaka.

Wasu basu son gaskiya, amma ba zan iya karya ba - Femi Adesina
Wasu basu son gaskiya, amma ba zan iya karya ba - Femi Adesina

Wannan Magana nashi na zuwa ne bayan yan Najeriya sun caccake shi akan lafiyan Buhari, wanda ke kasar Ingila yanzu domin jinya.

A ranan Talata, 7 ga watan Febrairu, Adesina ya fadawa tashar Channels Television cewa baya magana da Buhari kai tsaye amma wadanda ke tare da shin a cewa lafiyanshi kalau.

KU KARANTA: Kungiyar Boko Haram ta fada kwata- UN

“Ina Magana da Landan kullu yaumin, bance ina Magana da Buhari kai tsaye ba, amma ina tuntubar Landan kullum,ina Magana da mutanen da ke tare da shi.” Yace

Amma da dumi-dumi ya mayar da martini inda yace wasu mutane basu son gaskiya, amma irin wadannan mutane ba zasu sahi yayi karya ba.

A wata sako da yayi a shafinsa na Tuwita a ranan Laraba, 8 ga watan Febrairu, Adesina yace : “ Wasu sun fi son ayi musu karya. Amma wani kakakin ba zai musu karya ba. Nayi alwashin fadin gaskiya ko da kaka.”

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel