Wani gwamna ya kai ziyara asibiti, abun da ya gani zai baka takaici

Wani gwamna ya kai ziyara asibiti, abun da ya gani zai baka takaici

Gwamnan jihar Bauchi ya nuna takaicinsa bisa halin da ya tarar da babban asibitin jihar a ciki na rashin kayayyakin aiki da wajajen lura da marar lafiya.

Wani Gwamna ya kai ziyara asibiti, abun da ya gani zai baka takaici
Wani Gwamna ya kai ziyara asibiti, abun da ya gani zai baka takaici

Gwamnan wanda yakai ziyarar ba zata asibitin a ranar Litinin ya ce "abun takaici ne halin da na tarar da asibitin wanda Gwamnatin baya ta bayar da kwangila a gina sannan a sanya masa kayayyakin aiki na zamani, sai gashi na shiga na tarar wani dakinma ko tsinke babu "

Gwamnan M.A a saboda haka sai ya bukaci kwamishiniyar lafiya ta jihar da ta gaggauta duba abubuwan da asibitin ke bukata domin ya kawo agajin gaggawa, a yayinda yasha alwashin bin diddigin yadda yan kwangilar suka ci amana suka yi sama da fadi da dukiyar jama'ar jihar.

Yace: "Ba zan bar alummar jihata su cigaba da fuskantar kunci ba don haka zamu dauki matakan gaggawa akai."

Gwamnan ya kuma sha alwashin samar da makarantar unguwan zoma da kwalejin koyar da kiwon lafiya mallakin jihar domin kara ma'aikatan kiwon lafiya a asibitocin jihar,

Ya kuma sha alwashin daukar nauyin dalibai yan jihar zuwa kasashen ketare domin su koyo karatun likitanci su dawo jihar suyi aiki.

"Yanzu haka daga nan asibitin zan kai ziyara kwalejin koyon kiwon lafiya da Gwamnatin mu ke ginawa mallakin jihar Bauchi domin duba inda aikin yake gudana," inji Gwamnan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel