Uwar gidan 'Yar'adua ta bukaci yan Najeriya suyi wa Buhari addu'a

Uwar gidan 'Yar'adua ta bukaci yan Najeriya suyi wa Buhari addu'a

Mu sanya Shugaba Muhammadu Buhari cikin addu'a, Allah ya bashi lafiya, sakon uwargidan tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar'Adua.

Uwar gidan 'Yar'adua ta bukaci yan Najeriya suyi wa Buhari addu'a
Uwar gidan 'Yar'adua ta bukaci yan Najeriya suyi wa Buhari addu'a

Sakon Hajiya Turai 'Yar 'aduwa ga 'yan Najeriya

Hajiya Turai 'Yar 'aduwa ta bayyana hakan ne a shafinta na facebook, inda ta shawarci 'Yan Nijeriya da fadin alkari akan Shugaban da kaucewa furta munanan kalamai.

Shi kuwa Aliyu Tilde cewa yayi Allah ya bai wa Shugaban Kasa koshin lafiya, ya yafe masa kurakuransa da Zunubbanshi, ya shirye shi wajen shugabantar lamurranmu.

Shugaba a ko’ina abinda ya cancanta shi ne fada masa gaskiya a inda ake ganin ya yi kure; addu’ar shiriyar Ubangiji wajen shugabanci, da koshin lafiya da gafarar Allah.

A wani labarin kuma, Ministan watsa labarai, Lai Mohammed yace wannan gwamnati ba ta da wata shiri na boye ko ko a zahiri domin mai da kasa Najeriya kasar musulunci kawai.

Lai mohammed ya fadi hakanne a taron tattaunawa da mutane da akayi a garin Ilori, jihar Kwara.

Lai Mohammed ya ce wannan zancen kanzon kurege ne kawai domin babu irin wannan magana ko mai kama dashi lissafin wannan gwamnati.

Ya kara da cewa ‘yan siyasa ne kawai suke amfani da irin wadannan kalamai domin ingiza mutane da tada zaune tsaye a kasa Najeriya.

Shugabannin addinin Kirista da yawansu sun zargi wannan gwamnati da kokarin mai da kasa Najeriya kasar musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel