Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba

Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba

– Mai magana da bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karin haske

– Femi Adesina yace ko shi bai yi magana da Buhari ba a Landan

– Sai dai Adesina yace yana zantawa da na-kusa da shugaban kasa

Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba
Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba

Mai magana da bakin shugaban kasa Femi Adesina yayi karin haske game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Landan tare da kuma bayani a kan ranar da shugaban zai dawo.

Femi Adesina a wata hira da yayi a talabijin yace ko shi kan sa bai yi magana da shugaban kasar ba, sai dai ya kan yi magana da na-kusa da shi din. Adesina yace yak an tattauna da wadanda suke tare da shugaba Buhari a can Landan.

KU KARANTA: CAN ta caccaki Lai Mohammed

Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba
Mai magana da yawun shugaban kasa yace bai yi magana da Buhari ba

Mai magana da bakin shugaban kasar yace shugaba Buhari zai dawo kafin ma lokacin da ake tunani. Adesina ya kuma soki wasu da ke ta kara ruruta maganar tare da daura laifin tabarbarewar kasar bisa kan tsohon shugaba Jonathan.

Babban Lauyan nan na kasa Femi Falana SAN ya soki shugaba Muhammadu Buhari game da al’amarin rashin lafiyar sa. Falana yace ya kamata ace ‘Yan Najeriya sun san halin da shugaban su yake ciki.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel