HOTUNA: Paul Pogba ya siya katafaren gidan alfarma akan naira biliyan 1 da miliyan 300
Shahararren dan wasan kungiyar Manchester United Paul Pogba ya sayi wani katafaren gida irin na alfarma akan kudi pan miliyan 2.9, kimanin naira biliyan guda da miliyan dari uku kenan.

Shi dai wannan katafaren gida dake tsakiyar kasar Ingila yaci kudinsa, inda aka ruwaito gidan na dauke da manyan dakunan kwana guda 5, kwamin wanka na zamani wato ‘swimming pool’ na ciki daki, daki buga wasannin da shakatawa, da dai sauran tarkacen dakuna rututu.

KU KARANTA: Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri
Tun bayan zuwansa kungiyar Manchester daga Juventus, Paul Pogba yana zama ne a wani Otel, inda a yanzu ya shafe watannin shidda a Otel din.

Sai dai bayan an sha faman neman gidan da yayi daidai da bukatar Paul Pogba, Pogba mai shekaru 23 ya gamsu da wannan gidan da aka sama mai, wanda da fari farashinsa ya kai pan miliyan 3.49, amma daga bisani aka sallama masa akan pan miliyan 2.9
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon gidan:
Asali: Legit.ng