Hukumar FIFA ta hukunta Najeriya

Hukumar FIFA ta hukunta Najeriya

– Hukumar kwallon kafa na Duniya FIFA za ta cigaba da hukunta Chris Giwa

– Dama can Chris Giwa da wasu suna cikin masu laifi

– Chris Giwa na rikici da Shugaban kwallo NFF na Najeriya

Hukumar FIFA ta hukunta Najeriya
Hukumar FIFA ta hukunta Najeriya

Kungiyar FIFA ta kwallon kafa na Duniya za ta cigaba da hukunta wasu Jami’an kwallon kafar Najeriya watau NFF. FIFA tace har yanzu ba ta yafewa Chris Giwa da sauran Jami’an Najeriya da ta samu da laifi ba.

Kungiyar FIFA ta Duniya ta kama Chris Giwa da wasu da rikicin shugabancin kujerarar NFF na Najeriya a baya. Sauran Jami’an da aka hukunta sun hada da Muazu Suleiman, Johnson Effiong, Fema Sani da Yahaya Adama.

KU KARANTA: An kama barayin shanu

Idan dai ba a manta ba Chris Giwa ya kalubalanci shugaban kwallon kafan Najeriya NFF watau Amaju Pinnick yace sam shine shugaba ba wani ba. Bayan nan ne FIFA ta Duniya ta takawa Giwa da mukarraban sa burki, aka kuma hana su shiga kowace irin harka ta kwallon kafa a Duniya.

Mun samu labari ‘Yan Majalisun Najeriya suna karar Gwamnatin kasar Amurka a Kotu inda suke neman gwamnatin kasar ta biya su kudi har dala biliyan $1. ‘Yan Majalisun sun ce Amurka tayi masu sharrin lalata da ‘yan mata.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel