Matashi dan shekara 20 ya lakada ma jami’in LASTMA dukan tsiya

Matashi dan shekara 20 ya lakada ma jami’in LASTMA dukan tsiya

Hukumar kula da muhalli da tabbatar da dokar hanya LASTMA, ta kama wani direba mai shekaru 20 da laifin yi ma jami’an hukumar dake aikin bada hannun dukan kawo wuka yayin dayake kan aiki.

Matashi dan shekara 20 ya lakada ma jami’in LASTMA dukan tsiya
Matashi dan shekara 20 ya lakada ma jami’in LASTMA dukan tsiya

Matashin direban mai suna Benjamin Archibong yayi ma jami’in LASTMA mai suna Olumide Omomoyesan duka ne yayin dayake tabbatar da dokar hanya a yankin Ajah na jihar Legas, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa a wurin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewar Archibong ya shiga komar LASTMA, kuma har ta gurfanar da shi gaban kotun majistri dake Ogba, sa’annan kuma ta kama motar bus mallakan direban da saboda daukan Fasinja ba’a inda ya kamata ba.

KU KARANTA: Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

Ana tuhumar direban ne da yi ma jami’in LASTMA duka har da fasa mai hanci.

Kaakakin LASTMA, Taofiq Adebayo ya tabbatar da kama direban inda yace “a ranar 31 ga watan janairu ne muka kama mai laifin, kuma mun kais hi gaban kotu kan tuhumarsa da aikata laifin cin zarafin jami’in gwamnati har ma da fada da shi.

“Sai dai wanda ake zargin Benjamin Archibong ya musanta zargin, inda kotu ta bada belinsa kan kudi naira dubu 100, daga nan sai ta daga sauraron karar zuwa 28 ga watan Feburairun 2017.

“Shugaban hukumar yace sun gurfanar da wanda ake zargin ne bayan samun shawara daga kwamishinan yansandan jihar Legas Fatai Owoseni.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon yadda aka lahanta wani jami'in LASTMA

Asali: Legit.ng

Online view pixel