'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai

'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai

Babban hafsan sojan kasa laftanar janar Tukur Yusuf Buratai yace nan bada dadewa bane sojoji dake bakin daga wajen yaki da yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa masi gabas zasu koma gida ga iyalansu.

'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai
'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai

Buratai ya bayyana haka ne ta bakin kwamandan ‘Operation safe haven’ Manjo janar Nicholas Rogers a yayin bikin wasannin sadar da zumunci na kasashen yammacin afirka (WASA) daya gudana filin fareti na shelkwatar rundunar soji ta 3 a garin Jos.

KU KARANTA: Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

Babban hafsan sojan wanda shine na 26 a tarihin sojin kasar nan ya bayyana cewar a shekaru 6 da suka gabata, rundunar sojin bata samu damar shirya wannan wasa ba saboda matsalar tsaro da suka addabi kasar, amma bikin na wannan shekarar na nuni da cewar an ci karfin yan ta’adda a Najeriya kenan, kuma zaman lafiya ya dawo jihar Filato.

“Ina tabbatar muku da cewar nan bada dadewa ba sojojin dake fafatawa da yan Boko Haram a Arewa maso gabas zasu koma ga iyalansu, ina rokon iyalan sojojin dasu kara hakuri.”

Daga karshe ya bukaci sojoji dasu kasance masu da’a da biyayya, tare da sadaukar da kawunan su ga aikin soja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel