Rikikin kabilanci ya dai-daita gidaje sama da 8,000 a Taraba

Rikikin kabilanci ya dai-daita gidaje sama da 8,000 a Taraba

Mutane sama da dubu takwas hare-haren Fulani makiyaya da ba kakkautawa kan kauyukan manoma bakwai cikin kwanaki takwas ya raba da muhallansu da yanzu ke zaman hijira a sansanoni hudu dake jihar Taraba.

Rikikin kabilanci ya dai-daita gidaje sama da 8,000 a Taraba
Rikikin kabilanci ya dai-daita gidaje sama da 8,000 a Taraba

Harin Fulani makiyayan ya shafi kananan hukumomi Ardo-Kola, Lau da Yoro da ya yi sanadiyyar Kona kauyukan kurumus ciki harda dabbobi da anfanin gona da alkalumma suka yi kiyasan ya Kai na miliyoyin nairori.

Wannan na kunshe a bayanin ziyarar gani da Ido da mataimakin gwamnanm jihar Taraba Injiniya Haruna Manu da shugaban sashin tsaro na kwamitin wanzar da zaman lafiya a Arewa Maso Gabashin Najeriya Birgediya Janar Habila Vintanaba ya Kai yankunan da abin ya shafa inda mataimakin gwamnan ya yi alwashin nan ba da jimawa ba za’a maida su gidajensu tare da alkawarin dakatar da sake abkuwar lamarin.

Bayan ya kewaya yankunan da abin ya shafa Birgediya Janar Habila Vintanaba shugaban sashin tsaro na kwamitin wanzar da zaman lafiya a Arewa Maso Gabashin Najeriya ya yi Allah wadai da hare-haren lokacin da yake amsa tambayar dalilan yin anfani da jiragen sojan sama wajen dakile hare-haren.

Wani mazaunin Bandawa Vinnan daya daga cikin kauyukan da ke makwabtaka da wadanda aka kona Danjuma Bako ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna cikin wani hali na zaman zullumi da fargaban dalilan da ya suna nemawa yara da mata mafaka a yashin sifirin kogin binuwai don kaucewa harin da ake kaiwa kauyukan manoman.

Alamar tambaya ita ce ko me yasa yankin da ke fama da tashe-tashen hankulan ba zai kwaikwayi hikimar da yankin Gembu da suke jiha daya ke anfani da ita ba wajen samarwa kanta dawamammiyar zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel