Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

A ranar talata 7 ga watan Feburairu ne jami’an rundunar tsaron farin kaya wato Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Borno suka dakile yunkurin wasu yan mata su biyu yan kunar bakin wake da sukayi yunkurin kustawa cikin jerin motocin dake layi a gidan sayar da man fetur na NNPC a garin Maiduguri.

Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri
wanda aka kama

Kwamandan rundunar Ibrahim Abdullahi ya shaida ma kamfanin dillancin labarai (NAN) cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:45 na safiyar yau, Talata 7 ga watan Feburairu. “jami’an mu dake jibge a gidan man sun dakile yunkurin wasu yan kunan bakin wake daga kai harin bom a gidan man.

KU KARANTA: Hukumar kula da tashoshi jiragen ruwa, NPA, ta jinjina ma Kwastam

Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri
wanda aka harba a kafa

“yan matan su biyu sunyi yunkurin kutsawa cikin jerin motocin dake layin jiran mai ne, sai dai daya daga cikin maharani ta firgita bayan data kura jami’an mu sun ankara da ita, nan da nan ta cire rigar bom din tayi wurgi da shi, wannan ya bamu damar cafke ta cikin sauki nan take.

Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri
Rigar bom din data yar

“ita kuwa dayar, sai ta ruga tana kokarin shiga cikin jama’a, amma mun samu nasarar harbinta a kafa, inda ta fadi, ba tare da bom din ya tashi ba. A yanzu haka mun aika da jami’an mu kwararru akan warware bom.” Inji kwamanda Ibrahim Abdullahi.

Kwamandan ya kara da cewa tsirarun yayan kungiyar Boko Haram da suka rage suna kokarin samun damar kai hari a inda ba’a zata ba, don haka ya ja hankalin jama’a dasu sanya idanu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel