LABARI DA DUMI-DUMI: Mun ji koke-koken ku zarai – Inji Osinbajo

LABARI DA DUMI-DUMI: Mun ji koke-koken ku zarai – Inji Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya furta cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na iya kokarin ta na gani cewa ta inganta ruyuwa 'yan Najeriya.

LABARI DA DUMI-DUMI
Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji kukan 'yan Najeriya bayan wata zanga-zanga da aka gudanar a fadin kasa.

A cewar Osinbajo, Buhari wanda yake a halin yanzu a kan hutu na kula da lafiyarsa, ya yi alkawari cewa yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya gwamnatinsa zai yi duk iya kokarin ta saboda inganta rayuwa ral’umma, jaridar Punch ta rahoto.

Osinbajo ya sanar da wannan labara ne a wata dandali akan farfadowa da tattalin arzikin da kuma ci gaban Shirin gwamnati wada aka gudanar a fada shugaban kasa a Abuja, babban birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwan 5 da zai faru idan Buhari bai dawo ranar Litini ba

Ko da yake, mukaddashin shugaban kasar ya amince cewa al'umma na cikin wata hali mai tsanani sanadiyar durkushewar tattalin arziki da ake ciki, ina mai sheda maku cewa shugaban kasar ya amince da damuwar ku.

Zaku iya tuna cewa kwararen mawakin nan 2baba ya sanar da cewa za ayi wannan babban zanga-zanga na nuna rashin amincewa da gwamnatin tarayya a yau, 6 ga watan Fabrairu,2017.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel