Yadda kasuwancin 'Ponzi Scheme ya kusa rusa min rayuwata

Yadda kasuwancin 'Ponzi Scheme ya kusa rusa min rayuwata

- Wani dan kasuwa ya bayyana yadda ya yi hasarar sama da naira miliyan 2 hanyar nau'o'in zuba jarin 'ponzi scheme' daban-daban

- Matashin dan kasuwan ya rubuta labarinsa tare da domin ya zama darasi ga masu rawar kafar shiga MMM

Yadda kasuwancin 'Ponzi Scheme ya kusa rusa min rayuwata
Yadda kasuwancin 'Ponzi Scheme ya kusa rusa min rayuwata

A watan Oktoba 2016 na yi asarar dala 1,000 da na zuba jari a Ponzi Scheme wanda wani abokina ya nuna min MMM United.

Tun da fari na bada gudunmawar dala 200, sannan yayin da na ga hujjar biyan kudinsu sai na zuba jarin dala 1,000.

To bayan biyan su kudin ne akai rashin sa'a damar shiga yanar gizona ya kare kuma bana wajen da zan iya sabuntawa, katin cire kudi na ATM baya tare da ni sannan ofishin su a rufe da sauransu. Saboda haka ba abinda zan iya yi a lokacin.

Washegari na garzaya na sabunta damar shiga yanar gizon. Abin mamaki su ka hana ni damar shiga tsarin. Na yi duk abinda zan iya yi amma abin ya ci tura. Haka nan dala 1000 ta bi shanun sarki. Na bar abin a zuciyata.

A dai cikin wannan watan na Oktoba, na yi asarar dala 500. Wani abokina wanda na ke girmamawa sosai kuma zan ci gaba da girmamawa har illa masha'allahu ya nuna min 'Helping Revolution' (HR). Ya fada min su na da gaskiya da rikon amana.

Cewa zan iya zuba jari a bitcoin na samu ninkin abinda na zuba cikin kwanaki 7. Saboda amincewar da na yi masa da kimarsa a idona sai na amince na zuba jarin tare da su.

Biyo bayan haka na sayi bitcoin na dala 500 a tsarin 540 duk dala 1, na zuba kudin ga HR. Bayan kwana 2 sai ta bayyana 'yan damfara ne su ka tsere da kudina. Amma wancan duk labari ne.

A watan Nuwambar shekarar 2016 na yi asarar dala 700 a gurin MMM na Afrika ta kudu, wani abokina ne a nan Facebook ya nuna min wannan dandalin.

Ya bani shawarar zuba kudi a ciki zan samu kashi 150 na abin da na zuba a kwanaki 90, wayo na ya sa na zuba dala 700, har sai da aboki na ya gargade ni a kai, amma ban saurare shi ba tun da na saba taren aradu da ka. A kwana na 90, ina shirin fitar da kudi, amma ina!

Na karshe - MMM Nigeria. Na zabi na sa kudi Naira dubu 200, 000 na ba da wadannan kudi don na samu riba da ikon Allah.

A watan Nubamba, na yanke shawarar zuba Naira 500,000 a MMM Ponzi Scheme. Yanzu Disamba 2016 ta zo lokacin da zan girbi riba, amma aka yi rashin sa a, a tsakar daren ranar Litinin da Talata, MMM Nigeria su ka rufe account din kowa daga samun taimako. Ta haka na yi asarar naira dubu 500.

Ku biyo mu a shafin mu na Facebook a http:www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel