Buhari zai anshi filin jirgin saman Ummaru Musa

Buhari zai anshi filin jirgin saman Ummaru Musa

Gwamnatin Jihar Katsina ta nuna aniyarta na ba da goyon baya ga Gwamnatin Tarayya game da kokarin karbar ragamar tafiyar da filin jirgin sama na tunawa da Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Buhari zai anshi filin jirgin saman Ummaru Musa
Buhari zai anshi filin jirgin saman Ummaru Musa

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka ne a lokacin wata ziyara da Ministan Sufurin Jiragen Sama na kasa, Hadi Sirika ya kai ma shi ziyara. Gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar a shirye take ta tabbatar da ganin ana cikakken amfani da filin jirgin saman na Katsina.

Ya kara da cewa Shugaban Kasa Muhammad Buhari, shugaba ne da ya yarda da yin adalci ga sassan kasar nan game da kowane irin batu da ya shafi jindadin al’ummar kasar.

Tunda farko Ministan Sufurin Jiragen Saman, Sanata Hadi Sirika ya bayyana filin jirgin saman na Katsina da cewa yana daya daga cikin filayen jiragen sama masu inganci, shi ya sa aka zabi a karbe shi ya koma karkashin kulawar Gwamnatin Tarayya.

Sanata Hadi Sirika ya ce Gwamnatin Tarayya a shirye take ta maida filin Jirgin saman ya zama ana amfani da shi kamar yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel