‘Yan Boko Haram sun kwace wata gari a Yobe

‘Yan Boko Haram sun kwace wata gari a Yobe

Wasu mambobi kungiyar yan tada kashin bayan Boko Haram sun kwace garin Sasawa, wata gari a jihar Yobe da suka far ma bayan musayan wuta da rundunar sojin Najeriya a ranan Lahadi, 5 ga watan Febrairu.

SABUWA: ‘Yan Boko Haram sun kwace wata gari a Yobe
SABUWA: ‘Yan Boko Haram sun kwace wata gari a Yobe

Duk da cewa rundunar sojin Najeriya bata tabbatar da wannan labara ba, wata rahoton jaridan Daily Post tace yan ta’addan sun far ma garin da ke da kilomita 30 da babban birnin garin Damaturu, a motoci da Babura.

Duk da cewan an fitittiki yan ta’addan daga dajin Sambisa, har yanzu basu gushe suna kai farmaki garuruwan mutane a yankin arewa maso gabas ba.

KU KARANTA: Ya kamata a kara kudin masu bautan kasa zuwa 50,000- Fayose

Rahoton ta samu maganganu daga hannun mutanen garin wadanda suka tabbatar da cewa yan ta’addan sun far ma garin da yammacin ranan Lahadi kuma sun fitittiki soji.

Wani mazaunin garin yace a Damaturu yace : “Mazauna sun arce domin neman kariya yayinda yan ta’adda suna tayar da bama-bamai kuma suna harbin kan mai uwa da wabi.”

Rahoton tace an tura rundunar sojin Najeriya zuwa garin yanzu.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel