Sanata ya sa an daure wani dan siyasa a Kano

Sanata ya sa an daure wani dan siyasa a Kano

- Ana zargin Sanata mai walkiltar Kano ta arewa a majalisar dattijai da sa a kama tare da tsare wani matashin dan siyasa a bisa wasu kalamai da ya yi agidan rediyo

- Cikin kalaman da aka ce Dan siyasan ya yiwa Sanatan har da tonon silili na zargin sauya karamar hukumarsa

Sanata ya sa an daure wani dan siyasa a Kano
Dangawan jingau wanda ya gamu da fushin Sanata a Kano

Ana zargin dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta arewa Barau Jibrin da sa a kama da kuma tsare wani dan siyasa kuma sojan baka Yakubu Dangawan Jingau a bisa wasu kalamai da ya yi a gidan rediyo na batanci.

Cikin kalaman da batancin da da ake zargin dan siyasan sun hada da tuhumar asalin karamar hukumar haihuwar Sanatan ta Kabo.

Sanata Jibrin ya takararsa ta farko zuwa majalisar wakilai a shekarun 1999 zuwa 2003 ya tsaya takarar ne a karamar hukumar Tarauni daga baya kuma a cewar mai zargin, ya koma karamar hukumar Kabo wacce yanzu yake waklilta a majalaisar dattijai.

Sai dai a cewar, jaridar Daily Nigerian mai yada labaranta a intanet, bala'irar Danagawan ta soma ne a lokacin da ya zargi Sanatan a wani shirin siyasa da wani gidan rediyo mai zaman kansa ya ke yi a inda ya ce Sanatan ya yi watsi da 'yan mazabarsa.

Amma a cewar, wata majiya ta kusa da Sanatan wanda kuma shi ne shugaban kwamitina kulada albaraktun mai fetur, ta ce babban abin da ya fusata sanatan shi ne zagin matasahin na cewa, ya kasa biyan kudin kai wani bijimin Sa zuwa garin Minna wurin yayan sanatan. ya kumakara da zai bi sawun ya ga ko menen za a yi da bijinmin a can. wanda a cewar majiyar, na nufin wani abu kamar tsafi.

Kwana guda da yin wadannan kalamai a shirin rediyon ne, wasu jam'in tsaro na farin kaya suka yi awon gaba da matashin

Jaridar ta ce an tsare Dangawan har na kwanki 4 kafin a gurfanar da shi a gaban babban kotun Shariah da ke zama a Jigirya a ranar Juma'a 4 ga watan Fabarairu a inda aka tuhume shi da laifin yin kazafi da kuma cin zarafi, wanda ya musanta.

Kotun Alkali Abubakar Khalid ta ki bayar da belin matashin duk da roko da lauyansa Abdullahi Ibrahim ya yi na cewa laifin na cikin wanda za a iya bayar da beli, ta kuma sa ranar Laraba 8 ga watan Fabarairu don ci gaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a Facebook a www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel