Amurka ta yi Allah wadai da hare-hare kan kiristocin Najeriya

Amurka ta yi Allah wadai da hare-hare kan kiristocin Najeriya

- Majalisar wakilan Amurka ta ce an bayyana Najeriya a matsayin waje mafi hadari ga rayuwar kiristoci a duniya.

-Majalisar ta kuma ce kyale mutanen da su ka kashe kiristoci a Najeriya ba tare da an hukunta su ba na kara yawaita.

Amurka ta yi Allah wadai da hare-hare kan kiristocin Najeriya
Amurka ta yi Allah wadai da hare-hare kan kiristocin Najeriya

A wata takardar gayyata zuwa ga tsohon shugaba Goodluck, shugaban karamin kwamati kan Afirka da sha'anin lafiya na duniya da kare hakkin dan adam, Christopher Smith ya ce kashe kiristoci na kara bazuwa."

Jaridar This Day ta rawaito cewa Smith ya ce, karamin kwamitin ya binciko tashe-tashen hankula da dama da Najeriya ta fuskanta.

Ya ce shi da kansa da daya daga cikin ma'aikatansa, Greg Simpkins sun sha ziyartar Najeriya kuma sun yi magana da shugabanni addini a kan rikice-rikicen da ke faruwa a kasarnan.

Smith ya ce:

"Ni da daraktana na ma'aikata, Greg Simpkins mun ziyarci Najeriya a lokuta da dama inda mu ke tattaunawa da shuwagabannin addinan kirista da na musulunci a fadin kasar kuma mun ziyarci coci-cocin da aka kona ko aka jefa wa bom misali kamar a Jos.

"Abin bakin ciki, an bayyana Najeriya a matsayin waje mafi hadari ga rayuwar kiristoci a duniya sannan kuma hukunta wadanda su ke da alhakin kashe kiristoci na qara ta'azzara."

Ya bukaci tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya cika kudirin gidauniyarsa ta hanyar dabbaka dimokaradiyya da zaman lafiya da kawo canji a Najeriya.

"Ina gayyatar ka da ka zo Amurka sati mai zuwa ka bayyana mana ra'ayoyin ka game da wannan takaddama."

Wanda ya hada da zargin musuluntar da gwamnati karkashin gwamnati mai ci sannan da aikin da gidauniyarka ta shirya yi wajen hakuri da juna kan addini da kuma 'yanci," a cewar Smith

Juriyar da ka nuna wajen mika mulki ta nuna jajircewa sha'anin dimokaradiyyar kasarka da kuma tsayuwar kasar da kafafunta wadda shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya yabawa," ya fada

Tsohon shugaban ya yi jawabi ga karamin kwamitin ranar Laraba 1ga watan Fabrairu. A cikin abubuwan da aka tattauna da kwamitin su ne aiwatar da taron kasa na 2014 da ci gaba da kashe kiristoci a kudancin Kaduna da sauransu.

A nasa martanin Musa Abdullah wani mai sharhi kan al'muran yau da kullum a dandalin sada zumunta da muhawarana Facebook ya ce, Amurka ce ta fi kowacce kasa hadari ga musulmi a duniya sanna ya kuma ce,

Shin Amurka ta taba gayyatar wani mutumin Falasdinu dan yayi jawabi akan ukubar da "yan kasar sa suke sha a hanun Yahudawa 'yan kama-guri-zauna na Isra'ila? Hakan ba zai taba faruwa ba dan kuwa Isra'ila tana hallaka Musulmai ne a madadin America".

Sannan marubucin ya ci gaba da tambayar cewa, "Shin wa ya mayar da Siriya ta zama ta gagari Musulmi ya zauna ciki? Wa ya daidaita kasar Libya? Wa yake kokarin wargaza kasar Yemen?

Kasar America wadda bayan taimakawa wajen ruguza kasar Zaire ta kirkiro kungiyoyi masu fada da juna dan tayi amfani da hakan wajan sace albarkatun kasar?

America wadda ta wargaza tsarin gudanar da kotu irin na Musulunci a kasar Somalia dan ta tabbatar da cigaba da zubar da jini a kasar?

Yayin da gidan Rediyon BBC ya ke gabatar da wani shiri akan cin zarafin jama'a, daga cikin wadanda abun ya shafa da ta fara magana, wata mace ce da ta kira kanta Kirista"yan kasar Iran mai bin darikar Katolika.

Idan da gaske ne cewa Musulmai na kuntatawa Kiristoci a Najeriya, me yasa kurkukun kare-kukan ka na Guantanamo Bay da Abu Ghraib da sauran cibiyoyin gallazawa al'uma da America ta mallaka basu zama kan gaba ba wajen cirar tutar cin zarafin al'uma?

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya kamata ka roki damar zuwa ka fuskanci Majalisar dokokin America ka gaya musu yanda mu duka"yan Najeriya Musulmai da Kiristoci muka yarda cewa America tayi kokarin mayar da Najeriya gurin zama mai hadari ta hanyar daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana ra'yoyinsu dangane da wannan matsayi.

Kai za ka iya aiko da na ka a shafinmu na Facebook a htpp://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel