Malamin Izala ya nemi a daina bara

Malamin Izala ya nemi a daina bara

– Kungiyar Izala tayi tir da kalaman Fasto Sulaiman yana nema a zauna lafiya a Kasa

– Sheikh Jingir ya kuma nemi a daina bara a Najeriya

– Babban Malamin yayi kira ga shugaban kasa da ‘Yan Najeriya

Malamin Izala ya nemi a daina bara
Malamin Izala ya nemi a daina bara

Kamar yadda muka kawo maku rahoto dazu, Kungiyar nan ta Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta soki masu kirawa shugaba Buhari mutuwa. Wani babban Malamin Kungiyar ya kuma yi tir da kalaman Fasto Johnson Sulaiman.

Shugaban Majalisar Malamai na Kasa na Kungiyar ta Izala Sheikh Sani Yahaya Jingir yace kalamai irin na Fasto na iya tada fitina a Najeriya. Faston dai yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe duk wani Musulmi da suka gani kusa da cocin sa. Hakan ta sa har Hukumar DSS ta zauna da wannan Fasto.

KU KARANTA: Wani Babban Fasto ya musulunta a Ingila

Dattijon Malamin ya kuma yi kira da a daina tura kananan yara wurare masu nisa da sunan bara. Malamin yace ana amfani da yaran ta inda ba su dace ba saboda karancin shekarun na sau da dama.

Malamin har wa yau ya ba Gwamnati shawarar ta dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen yunwa da talauci da ake fama da su a halin yanzu.

Muna nan a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel