Ya rotsa kan matarsa bayan ya gano tana dauke da cutar ƙanjamau

Ya rotsa kan matarsa bayan ya gano tana dauke da cutar ƙanjamau

Wani matashi mai suna Titus Mabvuregudo ya hallaka matarsa a kasar Zimbabwe ta hanyar rotsa mata kai da dutse bayan ya gano tana dauke da kwayar cutar kanjamau, kuma ta harbe she da cutar.

Ya rotsa kan matarsa bayan ya gano tana dauke da cutar ƙanjamau

Hakan ya faru ne kuwa yayin da asirin matar ya tonu daidai lokacin damutumin ya ga kwalayen magungunan da take sha don kwantar da ciwon, nan fa suka shiga cacar baki mai zafi, wanda yayi sanadiyyar mijin ya kai mara hari, har ma ya hallaka ta.

Yansanda sun kama Titus Mabvuregudo inda suke tuhumarsa da kashe matarsa Rejoice Balewa, kuma mahaifiyarsa tace itace shaida.

KU KARANTA: In da ranka, ka sha kallo: ......Ta haifi kwaɗo

Kaakakin yansandan yace: “mahaifiyar wanda ake zargi wanda a gabanta akayi komai ta bayyana cewar daga cacar baki ne ya kashe matar tasa.”

Rahotanni sun bayyana cewar mahaifiyar tayi iya bakin kokarinta na ganin ta hana dan nata kashe matarsa, amma ina, tsohuwa bata san yaron nata karfi ke garai kamar talauci, inda cikin dan kankanin lokaci ya rotsa kan matar, kuma ya binne ta a wata gona.

Sai dai daga bisani mijin matar ya amsa laifinsa na kashe matarsa, inda yace ya dauki wannan mataki ne bayan ta shafa masa ciwon kanjamau.

A yanzu dai yana nan yana jiran hukuncin kotu, inda ake zarginsa da laifin kisan kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel