Darajar Naira za ta farfado

Darajar Naira za ta farfado

– Darajar Naira za ta farfado don kuwa CBN na shirin sa baki a lamarin

– Babban Bankin CBN zai yi wani abu na kokarin ganin yadda Darajar Naira za ta dan tashi

– Dala ta kai Naira N500 a kasuwar canji

Darajar Naira za ta farfado
Darajar Naira za ta farfado

Babban bankin kasar nan watau CBN na kokarin ganin yadda za ayi darajar Naira ta dan tashi. Yanzu haka da muke hada wannan labari dai Dalar Amurka guda ta kai kusan N500 a kasuwar ‘Yan canji.

Rahotanni da suke shigowa sun nuna cewa Bankin na CBN na shirin kawo karshe ko ragin karancin dalar da ake samu. Yanzu fad alar ‘foun’ ta kai har N615 yayin da kuma Dalar EURO ta ke kan N525.

KU KARANTA: Osinbajo ya kara ganawa da Saraki da Dogara

CBN dai za ta saki wasu Dala Miliyan 600 domin kawo sauki wajen karancin dalar da ake fama da ita. Wannan zai kawo sauki kanar yadda wani Ma’aikacin Bureau De Change na ‘Yan-canji ya bayyana.

A babban bankin dai farashin Dalar na kan N315 ne, sai dai a kasuwar ‘yan canji abin fa ba a cewa komai. Bankin CBN din dai a wannan makon tace ba ita ke sa farashin dala a kasuwa ba, CBN tace tuni ta saki farashin ya kada inda kasuwa ta yi da shi.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel