Jirgin yakin Najeriya ya dawo daga Gambia

Jirgin yakin Najeriya ya dawo daga Gambia

– Sojojin Najeriya sun dawo gida bayan an sauke Shugaba Jammeh

– Sojin Kasar sun dura Kasar Gambia ne lokacin da ake cikin halin rikicin siyasa

– Barrow ya fara aiki a matsayin shugaban kasa

Jirgin yakin Najeriya ya dawo daga Gambia
Jirgin yakin Najeriya ya dawo daga Gambia

Sojojin Najeriya sun dawo gida bayan an tuge Shugaba Yahaya Jammeh. Sojojin Najeriyar suna cikin Dakarun Nahiyar da suka dura Kasar Gambia gudan kar-ta-kwana watau ko da Shugaba mai-ci Jammeh yayi taurin kai.

Najeriya dai ta tura zuga guda Kasar domin tabbatar da cewa an nada Adama Barrow matsayin shugaba bayan ya lashe zaben da aka yi. Hakan kuwa aka yi don yanzu har sabon shugaban kasar ya sa aiki.

KU KARANTA: Yan Sanda za su shiga zanga-zanga

Tuni Barrow har ya canza sunan Kasar ta Gambia, ya cire Kasar Musuluncin da tsohon shugaba Sheikh Jammeh ya kakaba mata. Barrow ya zabi wata tsohuwar Ministar Jammeh a matsayin Mataimakiyar sa, ko da dai shekarun ta sun wuce yadda dokar Kasar ta kayyade.

An dai ga Sojojin Najeriya suna sintitiri yayin da Jammeh ya shigo Kasar ta Gambia daga Sanagal inda ya labe bayan zabe. Dakarun ECOWAS dai suka matsawa Jammeh har sai da ya sauka daga mulkin bayan ya fadi zabe, ba dan yana so ba. Jammeh ya fi shekaru 20 yana mulkin Kasar Gambia.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel