An guntule min hannu da kafa saboda ina son ina in mika wuya, dan Boko Haram ya bayyana

An guntule min hannu da kafa saboda ina son ina in mika wuya, dan Boko Haram ya bayyana

A yau Alhamis ne wani dan Boko Haram, Muhammad Abubakar, yace an guntule masa hannaye da kafa saboda yana shirin mika wuya ga rundunar soji a dajin Sambisa.

An guntule min hannu da kafa saboda ina son ina in mika wuya, dan Boko Haram ya bayyana
An guntule min hannu da kafa saboda ina son ina in mika wuya, dan Boko Haram ya bayyana

Muhammad Abubakar, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a wata hira da yan jarida wanda kwamnadan tiyata, Manjo Janar Lucky Irabor yayi.

KU KARANTA: Saraki,Dogara,Osinbajo na ganawa karo na 2

Muhammad Abubakar, yace na azabtar da shi ne saboda ya yanke shawaran cewa zai fita daga kungiyar yan Boko Haram kuma zai rungumi zaman lafiya. “ Na fadawa wani abokina, Hassan Dan-Guduma, cewa ina son mika wuya saboda na gaza gane manufar kungiyar.

“Da farko Hassan Dan-Guduma ya yarda da shawara ta amma daga baya ya yaudareni. Bayan tattaunawanmu, ya dawo da wasu guda 3 wani na tabbatar ya fada musu shirinmu. Sunce ina shirin tona asiri ga gwamnati sai suka mini wannan abu.”

Bayan sun guntule mini hannaye da kafa, sun jefani cikin kwalbati raina hannun Allah, har lokacin da soji suka zo suka ceceni.”

Manjo Janar Lucky Irabor yace: “Kun dai ga abinda sukayi ma dan uwansu saboda ya bar su”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel