Frank Lampard yayi sallama da kwallo

Frank Lampard yayi sallama da kwallo

– Tsohon Dan wasan Chelsea Frank Lampard ya ajiye kwallon kafa

– Frank Lampard ya ajiye wasa yana da shekaru 38

– Tsohon Dan wasan yana so ya koma harkar horarwa

Frank Lampard yayi sallama da kwallo
Frank Lampard yayi sallama da kwallo

Babban Dan wasan nan na Ingila Frank Lampard ya ajiye wasan kwallon kafa bayan yayi shekara da shekaru ana gwabzawa da shi. Lampard dai ya dauki fiye da shekaru 20 yana taka leda a Kasar Ingila da kuma Amurka.

Lampard ya fara bugawa Chelsea tun a shekarar 2001 bayan ya baro Kungiyar West Ham, sai da ya kai har shekaru fiye da goma a Kungiyar. Frank Lampard ya kuma bugawa Kasar sa ta Ingila kwallo na kusan shekaru 15.

KU KARANTA: Matsalar tattalin arziki na ta kara kamari

Dan wasa Lampard ya kafa tarihi inda ya fi kowa cin kwallaye a Chelsea, Lampard duk da dan wasan tsakiya ne ya ci wa Chelsea kwallayen da ba a taba samun irin su ba. Lampard ya zurawa Chelsea kwallaye 211; wanda ya fi na duk wanda ya taba bugawa Kulob din.

Lampard ya sanar ta Facebook cewa daga yanzu ya aijye tamula yana kuma mai alfahari da sunan da yayi. Lampard ya ci kwallaye kimanin 300 a fadin wasan rayuwar sa. Da alamu Lampard zai dawo bangaren horas da ‘Yan wasa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Shin wanene Lampard?

Asali: Legit.ng

Online view pixel