Copa del Rey: Barcelona ta casa Atletico Madrid 2-1

Copa del Rey: Barcelona ta casa Atletico Madrid 2-1

- Barcelona ta doke Atletico Madrid a karawarsu ta farko ta wasan kusa da na karshe na cin kofin Copa del Rey a gidan 'yan Madrid din Vicente Calderon

- Luis Suarez ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na bakwai da shiga fili, sannan kuma Lionel Messi ya kara ta biyu a minti na 33

Copa del Rey: Barcelona ta casa Atletico Madrid 2-1
Copa del Rey: Barcelona ta casa Atletico Madrid 2-1

Sai dai Antoine Griezmann ya ba wa masu masaukin bakin kwarin guiwa a karo na biyu da za su yi a ranar Talata a Nou Camp, sakamakon kwallo daya da ya rama a minti na 59, wadda ya ci da kai.

Alaves da Celta Vigo su ne sauran kungiyoyin da suka kai wasan na kusa da karshe, inda za su yi wasansu na farko ranar Alhamis.

A wani labarin kuma, Real Madrid ta yi ban kwana da gasar Copa del Rey ta bana, bayan da Celta Vigo ta doke ta da ci 4-3 a karawa biyu da suka yi a wasannin daf da na kusa da na karshe.

A wasan farko da suka kara Celta ce ta ci Madrid 2-1 a Bernebeu, sannan kungiyoyin biyu suka tashi 2-2 a gidan Celta a ranar Laraba.

Celta ce ta fara cin kwallo bayan da Real ta ci gida ta hannun Danilo tun kafin a je hutu, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo.

Daniel Wass ne ya ci Celta ta biyu kafin daga baya Lucas Vazquez ya farke wa Madrid.

Source: Legit

Online view pixel