YANZU-YANZU! Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 3

YANZU-YANZU! Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 3

- Kakakin rundunar Sojin Najeriya Sani Usman yace mayakan Boko Haram da yawa ne suka sheka lahira yau a wata batakashi da suka yi da Sojin Najeriya yau

- A wata sanarwa da Sani Usman ya sanya wa hannu, yace sojojin Najeriya 3 ne suka rasa rayukansu a batakashin inda wasu 5 suka sami raunuka dabam dabam

YANZU-YANZU! Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 3
YANZU-YANZU! Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 3

Ya kara da cewa Sojojin sun kwato makamai masu yawa a hannun mayakan Boko Haram din da ya hada da motocin yaki, bindigogi da harsashai.

Anyi arangamar ne a lokacin da sojojin Najeriya ke cigaba da kakkabe sauran maboyan Boko Haram din a kauyukan Dulsa da Buk dake karamar hukuma, Damboa.

A wani labarin kuma, Jiya wata kotun soja a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno ta yankewa wasu sojoji biyu hukuncin dauri saboda ta samesu da laifuka da aka zargesu da aikatawa.

Birgediya Janar Olusegun Adeniyi shi ne shugaban kotun wanda ya yanke ma sojojin biyu hukuncin dauri a gidan kaso.

Kotun ta yankewa Hassan Adamu hukuncin shekaru bakwai a gidan kaso sakamakon laifin kisa da aka sameshi dashi amma kuma ba da gangan ba. An zargeshi da aikata laifin ne ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2015 sakamakon durkawa wani Umar Aka harsashai har sau biyu a kirjinsa a bakin kasuwar Litinin ko Monday Market. Nan take Umar Aka ya bar duniya.

Shugaban kotun yace kotun ta sameshi da laifin kisa ba da gangan ba maimakon kisa da gangan. Dalili ke nan da aka yanke masa hukuncin shekaru bakwai maimakon hukuncin kisa. Amma sai hukumomin soja sun tabbatar da hukuncin kafin a aiwatar dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel