SABON BAYANI: Ministan lafiya ya musanta da an gano maganin cutar Kanjamau

SABON BAYANI: Ministan lafiya ya musanta da an gano maganin cutar Kanjamau

– Ministan lafiya mai suna Farfesa Isaac Adewole ya musanta labarin da an gano maganin cutar nan ta Kanjamau a wata Jami’a da ke Najeriya

– A kwanakin baya, an bayar rahoto cewa wani Farfesa mai suna Maduike Ezeibe na Jami’ar Michael Okpara ta Jihar Abia yayi wannan bincike

– Farfesa Adewole ya bayyana cewa ba abu kamar maganin cutar kanjamau yanzu a duniya

LABARI DA DUMU-DUMI: An gano maganin cutar Kanjamau
LABARI DA DUMU-DUMI: An gano maganin cutar Kanjamau

Bayan shekara da shekaru ana bincike wani Farfesa mai suna Maduike Ezeibe a Jami’ar koyon aikin gona ta Michael Okpara ya gano maganin cutar nan da ta gagari mutane watau Kanjamau. A Turance kuma ana kiran ta HIV wanda ke zama AIDS idan ta rika.

Shugaban Jami’ar da ke Garin Umudike na Jihar Abia ya bayyana haka bayan ya tara manema labarai. Farfesa Francis Otunta yayi ikirarin cewa wani Malamin Makarantar ya gano maganin cutar da ke karya garkuwar jiki.

KU KARANTA: UNICEF za ta kawowa Najeriya dauki

Amma jaridar Punch ta bayar rahoto cewa Ministan lafiya Farfesa Adewole ya tura sako kan wayar mai magana da yawun sashen lafiyar kasa mai suna Misis Boade Akinola cewa:

''Ban san akwai maganin cutar Kanjamau ba. Kuma, idan mutum ya gano maganin, akwai hanyoyi, zai bi.''

LABARI DA DUMU-DUMI: An gano maganin cutar Kanjamau
LABARI DA DUMU-DUMI: An gano maganin cutar Kanjamau

Farfesa Maduike Ezeibe da yayi wannan bincike dai yayi bayanin matakan da ya bi, da kuma sakamakon da ya samu. Yayi amfani da sinadarin Aluminium Silicate da kuma Magnesium Silicate. Sai dai abin da ban mamaki musamman dai tun da Farfesa Ezeibe Likitan dabbobi ne, ita kuma Kanjamau garkuwar jikin Dan Adam ta ke karyawa.

Kwanaki Jaridar Huffington Post ta rahoto cewa yanzu haka an samo maganin Kanjamau kuma har an yi wa wani ma’aikaci a Kasar Birtaniya magananin wannan cuta, kuma ya warke.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel