Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000

Shugaban kasar Najeriya mai rikon kwarya, Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da fara amfani da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000 a kauyukan Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000

Farfesa Osinbajo ya kaddamar da shirin ne a kauyen Wuna dake karamar hukumar Gwagwalada na babban birnin tarayya a ranar Talata 31 ga watan Janairu, inda aka sanya ma gidaje 200 na’urar samar da wuta mai amfani da hasken rana, karo na farko.

KU KARANTA: Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Osinbajo yace gwamnati ta yanke shawarar neman sabbin hanyar samar da wuta ne bayan ta tabbatar da cewar babu kasar da zata samu cigaba ba tare da samun isashshen wuta ba, don haka ne ta fara shirin samar da wuta mai amfani da hasken rana ga talakawa marasa karfi, inda yace za’a samar da wannan wuta a gidaje 20,000 a duk fadin kasar a nan gaba kadan.

Shirin na samar da wuta daga hasken rana yayi daidai da manufar gwamnati na samar da isashshen wuta tare da kara masa karfi daga kashi 13 zuwa 23 a tsakanin shekarun 2025 da 2030.

Ana gudanar da aikin ne da hadin gwiwar kamfanin wuta na Neja Delta (NDPHC) da kamfanin kimiyya na Azuri. Osinbajo yace “muna da nufin gudanar da ayyuka manya manya daban daban da zasu kawo karshen matsalar wuta a Najeriya, musamman a kauyukan mu. Shugaba Buhari ya damu matuka dangane da inganta noma da ilimi a kauyuka.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wuta mai amfani da hasken rana a gidaje 20,000

“mun tattauna ta yaya zamu habbaka noman rani, samar da ingantattun kayyakin makarantu, don haka dole mu samar da injian ban ruwa, da sauran kayan aiki. Don haka muka yanke shawarar samar da wuta daga hasken rana saboda saukin amfaninsa da arha. da muka yanke shawarar yin hakan, sai muka tattauna da kamfanin Azuri.

“zamu fara da gidaje 20,000, amma muna fatan fadada aiki, hakan ya sanya muka fara shigo da kamfanunuwan yan kasuwa cikin shirin saboda muhimmancin hasken wutan rana.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel