‘Matukar ina raye, ba zan daina ɓaɓatu ba’ – Shehu Sani

‘Matukar ina raye, ba zan daina ɓaɓatu ba’ – Shehu Sani

Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya fallasa duk abinda suka tattauna yayin ganawarsa da shuwagabannin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Cif John Odigie Oyegun.

‘Matukar ina raye, ba zan daina ɓaɓatu ba’ – Shehu Sani
Shehu Sani

Sai dai ba kamar yadda jaridu ke yadawa ba, Shehu Sani yace uwar jam’iyya bata gayyace shi ba, amma a radin kansa ne ya kai mata ziyara a ranar Talata, inda yace jam’iyyar ta shaida masa bata da matsala da binciken sakataren gwamnati Babachir David Lawal da majalisa ke yi.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin daya sanya rikicin kudancin Kaduna karewa

Shehu Sani yace “uwar jam’iyyar APC ta roke ni dana daina babatun da nake yi, amma na shaida musu matukar ina raye ba zan daina babatu ba, kuma na shaida musu ni fa ban soki shugaban kasa ba. Amma nayi watsi da wasikar ta shugaban kasa saboda abu uku: an cire sunana a cikin wasikar, duk da matsayina na shugaban kwamitin binciken, na biyu kuma; sakataren gwamnatin ya musanta cewar mun gayyace shi, na uku kuma: wasikar tace wai ba’a samu rinjaye ba a kwamitin yayin daukan matakin.”

Kwamared ya cigaba da fadin “kamata yayi uwar jam’iyya ta gayyaci Babachir tunda shima ai ya bayyana aikin yan majalisa a matsyain aikin banza, kuma sun shaida min cewar sun basu goyon bayan kalaman da dukkanin mu biyu muka yi amfani dasu, sa’annan sun ja kunnen mu akan basu son muna kwance ma juna zani a cikin kasuwa.

Sanatan bai tsaya nan ba, yace “ na nuna musu bacin raina game da son kai da ake nunawa wajen yaki da cin hanci da rashawa, don haka ya kamata yan Najeriya su waye. Majalisa kuma zata fitar da cikakken rahoton binciken daya nuna almundahanar da Babachir ya aikata, kuma babu wanda ya isa ya hana mu gudanar da binciken satar kudaden yan gudun hijira.”

Idan ba’a manta ba shugaba Buhari yayi watsi da rahoton kwamitin majalisar dattawa wanda ta binciki badakalar satar kudaden yan gudun hijira, inda suka bukaci Buhari ya sallami Babachir sakamakon an kama hannunsa dumu dumu cikin bahallatsar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel