Gobara a kasuwan Balogun a jihar Legas

Gobara a kasuwan Balogun a jihar Legas

Wata shagon sayar da atamfa a sanannen kasuwan nan na Balogun a jihar Legas na ci bal-bal da wuta.

Wayo Allah: Gobara a kasuwan Balogun a jihar Legas
Wayo Allah: Gobara a kasuwan Balogun a jihar Legas

Game da cewar jaridan Premium Times, har yanzu ba’a san abinda ya jawo gobaran ba amma idanuwan shaida sunce wata injin jannareto ya tashi kafin gobaran.

Zuwa yanzu dai, ba’a samu rashin rayuwa ba ko kuma wanda ya jinkita, amma jami’an kashe wuta na nan suna kashen wutan.

KU KARANTA: Dan sanda yayi ma mace jina-jina

Wannan na faruw ne bayan wata kasuwa a Jimeta,garin Yola ,jihar Adamawa ta kama da wuta.

Game da cewar idon shaida, wutan ta fara ci ne karfe 7 na yamma bayan mutane sun gama siye da siyarwa sun koma gida, kuma an kulle kasuwa.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel