Gambia: An gano muggan makamai a gidan tsohon shugaba Jammeh

Gambia: An gano muggan makamai a gidan tsohon shugaba Jammeh

- Dakarun sojin Yammacin Afirka da aka tura kasar Gambia ta ce ta gano makamai a gidan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jammeh

- Kungiyar ECOWAS ta ce an gano makamai da harsasai ne a gidan Yahya Jammeh dake cikin kauyen Kanilai

Gambia: An gano muggan makamai a gidan tsohon shugaba Jammeh
Gambia: An gano muggan makamai a gidan tsohon shugaba Jammeh

Mista Jammeh ya bar kasar kwanaki 10 da suka wuce bayan da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da shugaba Adama Barrow ya yi nasara a watan Disambar bara.

Mista Barrow ya bukaci dakarun ECOWAS su zauna a kasar don tabbatar da kwanciyar hankali a lokacin da tsohon shugaban ya bar Gambia.

A wani labarin kuma, Sabon Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya tsame Kalmar 'Islama' daga cikin sunan da ake kiran kasar ta su.

A tattaunawa da manema labarai karon farko Adama Barrow ya kuma ce za'ayi sauye-sauye sosai wajen harkokin tsaron kasar, yayinda ‘yan jaridu za su sami ‘yancin walwala sosai.

Ya ce zai sauya sunan Hukumar tsaron kasar, wadda ta kunshi ‘yan sandan da ake jin tsoro saboda karfin iko da aka basu.

A shekara ta 2015 ne dai tsohon shugaba Yahya Jammeh ya sauya yadda ake kiran sunan Gambia ta zama janhuriyar Islama ta Gambia

Kashi 90% daga cikin mutan kasar dai musulmi ne.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel