Sabon rikicin kabilanci ya bulla a Taraba

Sabon rikicin kabilanci ya bulla a Taraba

- Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a rikicin jihar Taraba da ya barke yau Talata.

- Kamar yadda rahotanni ya zo, ‘Yan Kabilan Mummuye ne suka afka ma wadansu kauyukan Fulani da ya hada da garuruwan Lushi, Sakuwa , Ladde da Garin Dogo.

Sabon rikicin kabilanci ya bulla a Taraba
Sabon rikicin kabilanci ya bulla a Taraba

Gidaje da dama ne aka kona a rikicin Talata din.

Kamar yadda Hukumar ‘yan sandan Jihar Taraba ta sanar, wadansu matasa ne ‘yan asalin Kabilar Mummuye suka farma kauyukan Bonja, da Mayo-Kunga wanda garuruwan Fulani ne. Da ga nan ne kuma suma suka ne mi daukan fansa akan hakan in da har mutane goman suka rasa rayukansu a rikicin.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya umurci mutanen yankin musamman mabiya addinin kirista da su ta shi tsaye domin kare kansu akan hare-haren da basu ji ba basu gani ba.

Ya fadi hakanne a lokacin da yake jawabi akan rikin Kudancin Kaduna a Jalingo.

Hujumar ‘Yansanda ta tabbatar da hasaran gidaje sama da 75.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel