An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt

An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt

An kama matan guda biyu wadanda ake zargin yan fashi ne tare da makullaye wanda suke amfani dashi gurin yiwa mutane fashi.

An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An tissa keyar Favor da Uchechi kan laifin sata

A cewar wani rubutu da wani mai amfani da shafin Facebook Bright Jossy ya yada, an kama wasu barayi mata guda biyu, Favor da Uchechi, tare da makullaye wanda suke amfani dashi gurin yin fashi cikin nasara a makwabtansu.

An kama barayin ne a yankin Ada Goerge, Port Harcourt. Yan sanda sun tafi dasu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Da ya yada hotunan yan fashin, ya rubuta:

“An kama wasu gawurtattun barayi wadanda sukayi ikirarin sunayensu Favour da Uchechi daga Abia da jihar Imo, a unguwar Rumoke, kusa da Ada George Road, Port Harcourt tare da taimakon shugaban matasan Najeriya wato National Youth Council Of Nigeria (NYCN) babin jihar Rivers, Amb Sukubo Saraigbe Sukobo da wasu mambobin kungiyar bta NYCN da rana tsaka tare da mukullaye daban-daban, wanda suke amfani dashi gurin bude kofofin mutane dake makwabtansu idan sun tafi aiki da sha’aninsu nay au da kullun.

An mika su hannun hukumar yan sandan Najeriya, sashin Ada George.”

Kalli hotunansu a kasa:

An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An binciki dakin matan don gano abubuwan da suka sace
An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt
An hargitsa daki matan

Allah ya kyauta!

Asali: Legit.ng

Online view pixel