YANZU-YANZU! An sake kai hari masallaci a gaban jami'ar Maiduguri

YANZU-YANZU! An sake kai hari masallaci a gaban jami'ar Maiduguri

Labaran da suke iso mana yanzu-yanzu sun nuna cewa an samu wani dan kunar bakin wake da ya kusa kai cikin wani masallaci dake a unguwar Dalori a garin Maiduguri gaban jammi'ar Maiduguri da sallar asubar yau Talata inda kuma ya tada bam din da yake jikin sa.

YANZU-YANZU! An sake kai hari masallaci a gaban jami'ar Maiduguri
YANZU-YANZU! An sake kai hari masallaci a gaban jami'ar Maiduguri

Kamar dai yadda labarin ya iso mana ana tsoron cewa rayuka da dama sun salwanta yayin da wasu kuma suka jikkata.

Mai karatu dai zai iya tuna a kwanan baya ma dai Hukumomin tsaro a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane hudu sakamakon harin da aka kai a sanyin safiyar yau litinin a cikin harabar jami’ar garin Maiduguri da ke jihar Borno, kuma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wani mashahurin Shehin malami Farfesa Aliyu Usman Mani.

Ance harin kunar bakin wake ne aka kai inda mace da namiji suka tada bom din da ke jikinsu a cikin Masallacin gidajen Malamai da kuma kofar shiga Jami'ar.

Dan kunar bakin waken na farko ya shiga masallaci ne a cikin jami’ar inda ya tayar da bom.

‘Yar kunar bakin waken mace kuma ta yi kokarin shiga kofar jami’ar ne gate 5, tana kokarin haurawa wani jami’i ya harbe ta sai bom din ya tashi.

Wannan shi ne karo na farko da aka taba kai harin bom a cikin Jamiar Maiduguri.

Cikakken rahota na tafe..

Asali: Legit.ng

Online view pixel