Za’a sha biki, Messi zai auri budurwasa Antonella

Za’a sha biki, Messi zai auri budurwasa Antonella

Shararren dan wasan kwallon kungiyar Barcelona Lionel Messi ya daura damban auren budurwar sa da suka shafe shekaru 9 sun soyayya, kuma uwar ýaýansa guda biyu, Antonella Rocuzzo.

Za’a sha biki, Messio zai auri budurwasa Antonella
Za’a sha biki, Messio zai auri budurwasa Antonella

Rahotanni sun bayyana cewar an sanya ma masoyan ranar aure a 27 ga watan Yuni na shekarar 2017 da muke ciki, kuma za’a daura auren ne a can garin su Lione Messi, Rosario, a kasar Ajentina.

KU KARANTA:Manchester City na cikin babbar matsala saboda wannan dalilin (Karanta)

Hasashe ya nuna wannan biki zamo zakaran gwajin dafi a kasar Ajentina, sakamakon irin shirin da ake yi masa, inda ya za’a gayyace mutane sama da 600.

Za’a sha biki, Messio zai auri budurwasa Antonella

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Antonella ta haifa ma Lionel Messi yaya guda biyu, da suka hada da Thiago, mai shekaru 4, sai Mateo Messi dan shekara 1 da rabi.

Za’a sha biki, Messio zai auri budurwasa Antonella

Muma a nan, muna taya ango Messi da amarya Antonella murna.

Ku kalli bidiyon Messi da iyalinsa a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel