Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Kimanin mutane shida ne suka rasa rayukansu, takwas kuma suka jikkata yayin wani hari da wasu yan bindiga suka kai ma musulmai masallata yayin da suke sallar Isha’i a masallacin garin Quebec dake kasar Canada.

Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Haka ya sanya shugaban kasar ta Canada, ‘Prime Minister Justin Trudeau’ bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci akan musulmai da musulunci.

Sai dai yansanda sun bayyana cewar an kama mutane biyu da ake zargi na da hannun a cikin kai harin, amma basu bada cikakken bayani dangane da abin daya tunzura su kai harin ba.

Jim kadan bayan faruwar lamarin limamin masallacin ya bada adadin mutane biyar da suka rasu, yayin da wani shedan gani da ido ya bayyana cewar ya ga yan bindiga uku da idonsa yayin da suka bude wuta kan masallata da yawansu ya kai mutane 40 a cikin masallacin Quebec. Amma a rahoton yansanda sun ce yan bindigan su biyu ne kawai.

KU KARANTA:Bayan Trump ya alanta yaki da musulunci, an kona babban masallacin Texas

Kaakakin yansandan garin Quebec Christine Coulomb eta bayyana ma yan jaridu kamar haka, “mun tabbatar da mutuwar mutane shidda sakamakon harin, wadanda shekarunsu ke tsakanin 35-70, sa’annan kuma mutane 8 sun samu rauni, sai mutane 39 da suka sha ba ko kwarzane.”

Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Dayake limamin masallacin Mohamed Yangui baya cikin masallacin yayin da harin ya auku, amma yace jama’a da dama sun kira wayarsa a lokacin da lamarin ke wakana. “bamu san menene dalilin faruwar haka ba, wannan jahilci ne” inji shi.

Shima shugaban kasar Canada Justin Trudeau yace “mun yi tir da wannan harin da aka kai ma musulmai a cikin wajen idansu. Musulman kasar Canada na da matukar muhimmanci ga wannan kasar tamu, don haka ba zamu lamunci irin wannan aikin na rashin hankali ba a gruruwan mu, biranen mu da kasar mu gaba ki daya.”

Wannan hari ya auku ne daidai lokacin da shugaba Trudeau yace kasar Canada na maraba da yan gudun hijira, sakamakon korar kare da gwamnatin kasar Amurka ta fara yi musu, musamman ma kashe bakwai da shugaba kasar Amurka Donald Trump yayi ma Katanga daga shiga kasar ta sa.

Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Shima wani dan majalisar dokokin kasar Canada, Greg Fergus ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa “wannan aikin ta’addanci ne, wannan ya biyo bayan yawan bata musulunci ne da ake yi. Musamman ire iren zantukkan da kalaman batanci da ake furtawa.”

Gwamnan garin Quebec, Phillipe Couillard yace za’a karfafa tsaro a dukkanin masallatan garin Quebec da Montreal. Sa’annan ya jajanta ma al’ummar musulman kasar inda yace “muna tare da ku, kuma muna muku maraba a gidajen mu, dukkanin mutanen Quebec ne. ya zama wajibi mu cigaba da yin maraba da juna tare da zaman lafiya.

Haka zalika gwamnan garin New York Bill de Blasio ya tabbatar da karin tsaro ga dukkanin masallatan New York, shima yace “dukkanin al’ummar garin New York su kasance masu kula, da zarar kunga abinda baku gane mai ba, kuyi magana.”

A wani labarin kuma, shugaban kasar Faransa Francois Hollande yayi da wannan harin na Quebec cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin 30 ga watan Janairu inda yce “harin ta’ddancin nan hari ga zaman lafiyar garin Quebec. Kasar Faransa na jajinta ma mutanen da abin ya shafa, tare da iyalansu.”

Ita ma garin Quebec na fama ne da kwatankwacin matsalar kasar Faransa ke fama da shi sakamakon karuwar yawan musulman kasashen, duk da cewa kasashe ne marasa da addini. A watan Yunin daya gabata ma an ajiye kana lade a kan kofar shiga masallacin na Quebec.

Daya daga cikin masallata a masallacin Quebec Mohammed Oudghiri yace “shekaruna 42 a garin nan, amma a yanzu na fara shiga cikin damuwa, ina tunanin zan koma kasata Morocco.”

Ga bidiyon harin nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel