Sabon shugaba Barrow ya raba sunan Gambia da Musulunci

Sabon shugaba Barrow ya raba sunan Gambia da Musulunci

- Sabon Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya tsame Kalmar 'Islama' daga cikin sunan da ake kiran kasar ta su.

- A tattaunawa da manema labarai karon farko Adama Barrow ya kuma ce za'ayi sauye-sauye sosai wajen harkokin tsaron kasar, yayinda ‘yan jaridu za su sami ‘yancin walwala sosai.

Sabon shugaba Barrow ya raba sunan Gambia da Musulunci
Sabon shugaba Barrow ya raba sunan Gambia da Musulunci

Ya ce zai sauya sunan Hukumar tsaron kasar, wadda ta kunshi ‘yan sandan da ake jin tsoro saboda karfin iko da aka basu.

A shekara ta 2015 ne dai tsohon shugaba Yahya Jammeh ya sauya yadda ake kiran sunan Gambia ta zama janhuriyar Islama ta Gambia

Kashi 90% daga cikin mutan kasar dai musulmi ne.

A wani labarin kuma, Iran ta ce za ta mayar da martanin da ya dace kan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na hana Musulmi daga wasu kasashe 7 zuwa kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce za ta hana daukacin Amurkawa zuwa kasar saboda abinda ta kira cin zarafin da Amurka ta yi wa ‘yan kasar ta, har sai Amurka ta sake matsayi akai.

Rahotanni sun ce an hana ‘yan kasar Iran da Iraqi hawa jiragen da ke tafiya Amurka saboda umarnin shugaba Trump.

Kamfanonin jiragen Etihad da Emirates da Turkish airline sun ce an umurce su da kar su sayar da tikitin Amurka ga ‘yan wadanan kasashe 7 ko kuma barin 'Yan kasar ta Iran da ke dauke da fasfo din Amurka hawa jirgin da zai kai su kasar.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel